Rasha-Masar

Babu wanda ya tsira a hadarin jirgin Rasha

Wasu daga cikin 'yan uwan fasinjojin jirgin da ya yi hatsari.
Wasu daga cikin 'yan uwan fasinjojin jirgin da ya yi hatsari. REUTERS/Peter Kovalev

Hukumomin Rasha sun tabbatar da mutuwar ilahirin mutanen da ke cikin jirgin fasinjan kasar da ya yi hatsari a ranar asabar dauke da mutane 224 a yankin Sinai da ke kasar Masar.

Talla

Wata sanarwa da ofishin jakadancin Rasha a Masar ya fitar ne, ta tabbatar da haka, inda kuma ta ke dauke da sakon ta’aziya ga iyalan mamatan.

Ofishin Firaimistan Masar Sherif Isma’il ya ce, jirgin ya tashi ne daga wurin shakatawa na Sharm El-Cheik da ke Masar, inda ya nufi birnin Saint-Petersburg na kasar Rasha.

To a dayan bangaren kuwa, Kungiyar IS da ke Masar, ta yi ikirarin kabbabo jirgin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.