Jordan

Kungiyar Turai ta ba ‘Yan gudun hijira tallafi a Jordan

Sansanin 'Yan gudun hijira a kasar Jordan
Sansanin 'Yan gudun hijira a kasar Jordan REUTERS/Muhammad Hamed

Kungiyar Kasashen Turai ta sanar da shirin ba kasar Jordan euro miliyan 28 da ke hidima da dubban ‘yan gudun hijirar Syria da ke samun mafaka a cikin kasar.

Talla

Kwamishiniyar jinkai ta kungiyar Christos Stylianides ta sanar da tallafin a ziyarar da ta kai sansanin ‘yan gudun hijirar da ke Zaatari a Arewacin Jordan wanda ke dauke da mutane 800,000.

Tallafin yanzu ya kai adadin da kungiyar ta bayar zuwa miliyan 198 tun barkewar tashin hankalin Syria a shekarar 2011.

Za a yi amfani da tallafin domin hidima da ‘Yan gudun hijirar Syria a fannin kiwon lafiya da ilimi da samar da ruwan sha mai tsabta.

Kasar Jordan ta ce ta karbi ‘Yan gudun hijirar Syria kimanin miliyan 1.4.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.