MDD

Grandi zai jagoranci hukumar 'yan gudun hijira ta MDD

Filippo Grandi
Filippo Grandi Copyright : ONU/Filgueiras/Paulo

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya bayyana Filippo Grandi, jami’in diflomasiyar Italiya a matsayin wanda zai zama shugaban hukumar kula da yan gudun hijira. 

Talla

Grandi zai maye gurbin Antonio Guteres dan kasar Portugal wanda ya kwashe shekaru 10 yana jagorancin hukumar.

Kafin nadin na sa Grandi na rike da hukumar da ke kula da yan gudun hijirar Falasdinu yayin da ake sa ran a ranar 1 ga watan Janairu mai zuwa ne zai fara jorgorantar hukumar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.