Jamus

Jamus na leken asiri a Faransa da Amurka da MDD

Shugaban Faransa, Francois Hollande da Shugaban Amurka, Barack Obama da Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel.
Shugaban Faransa, Francois Hollande da Shugaban Amurka, Barack Obama da Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel. REUTERS/John Macdougall/Pool

Wani rahoton wata kafar yada labarai a Jamus ya zargi kasar da leken asirin Faransa da hukumar FBI da kuma hukumar UNICEF ta Majalisar Dinkin duniya da ke kula da ilimin yara kanana.

Talla

Wata kafar yada labaran Rediyo ce Inforadio a Jamus ta rawaito labarin da ke zargin hukumar leken asirin kasashen ketare a kasar na gudanar da ayyukan leken asirin ministan harakokin wajen Faransa Laurent Fabius da Hukumar ‘yan sanda ta FBI ta Amurka da kuma hukumar UNICEF ta Majalisar Dinkin Duniya.

A rahoton an zargi hukumar da nadar zantuka na wayoyoin salula da sakwannin email.

wannan kuma wani sabon al’amari ne ya bullo a Jamus, musamman ga shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel wacce a baya ta fada wa Amurka cewa bai dace aminnan juna na leken asirin junansu ba, bayan zargin Amurka na nadar zantukanta

Kafar yada labaran dai ba ta bayyana inda ta samu labarin ba.
Kuma baya ga UNICEF da FBI da Laurent Fabius, kafar yada labaran ta ce , hukumar leken asirin ta jamus ta yi leken asirin kotun hukunta laifukan yaki ta ICC da hukumar lafiya ta duniya WHO da wasu manyan kamfanonin kasashen Turai da Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI