Faransa

Taron G20 ya mayar da hankali kan harin Paris

Shugabanni  kasashen G20 a tsayuwarsu na shirun minti guda
Shugabanni kasashen G20 a tsayuwarsu na shirun minti guda REUTERS/Jonathan Ernst

Yayin da ake cigaba da zaman makoki da nuna alhini harin birnin Paris na Faransa, Shugabannin kasashen duniya 20 masu karfin tattalin arziki G20 sun tsaya shiru na minti guda domin nuna jimami harin da ya kashe mutane 129 tare da jikata sama da 300.

Talla

Shugaba Barack Obama na Amurka, Xi Jinping na China da Vladimir Putin na Rasha na daga cikin wadanda ke halartar taron G20 na bana a Turkiyya, wanda ya zo a cikin wani yanayi na tsanantar ayyukan ta’addanci da kuma rikicin Syria.

A na sa bangaran shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce Amurka za ta ninka kokarin da ta ke yi wajen kawo karshan mayakan ISSI a duniya.

Taron dai a yanzu ya fi mayar da hankali ne kan Harin Paris wanda bayan mutane 129 da suka mutu sama da 300 sun jikkata

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI