Faransa

Harin Paris na neman sauya makomar 'yan gudun hijira

Dubban 'yan gudun hijira ne ke neman mafaka  a kasashen Turai.
Dubban 'yan gudun hijira ne ke neman mafaka a kasashen Turai. Reuters

Mahawara ta kaure a kasashen duniya kan makomar ‘yan gudun hijirar Syria bayan aukuwar harin ta’addancin birnin Paris da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 129, bayan da aka samu daya daga cikin maharan dauke da fasfon kasar Syria. 

Talla

Shugaban majalisar wakilan kasar Amruka Paul Ryan ya bayyana bukatar dakatar da ci gaba da karbar ‘yan gudun hijirar kasar Syria da Amurka ke yi, bisa fargabar da ake da ita na samun kutsen mayakan jihadin a cikin ‘yan gudun hijirar.

Shi ma firaministan kasar Hugary, Viktor Orban da shugabar jam’iyar masu ra’ayin rikau ta kasar Faransa FN Marine Le Pen, sun bukaci dakatar da karbar ‘yan gudun hijirar kasar ta Syria a cikin kasashensu.

Sai dai tuni Majalisar dinkin duniya ta caccaki kiraye-kirayen na korar ‘yan gudun hijirar da ke neman iznin zama a kasashen na turai, inda ta ce wannan mataki ya yi nesa da zama mafita.

Kakakin Majalisar dinkin duniya Stephane Dujarric ya ce, ana iya fahimtar kasashen, cewa suna daukar matakai ne domin kare al’ummarsu daga dukkanin aikin ta’addanci, to amma korar ‘yan gudun hijirar abune da bai dace ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.