WHO

WHO ta bukaci taron Paris ya tattauna kan kiwon lafiya

WHO ta ce matsalar dumamar yanayi na sanadiyar mutuwar mutane da dama a duniya.
WHO ta ce matsalar dumamar yanayi na sanadiyar mutuwar mutane da dama a duniya. REUTERS/Ajay Verma/Files

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta bukaci mahalarta taron kasa da kasa kan sauyin yanayi da za a yi a birnin Paris na kasar Faransa a wannan wata, da su mayar da hankali kan yadda za a magance matsalolin kiwon lafiya da ke da nasaba da illolin sauyin yanayi.

Talla

Hukumar ta bayyana cewa matsalar dumamar yanayi ita ce babban dalilin da ke haddasa asarar dubban rayukan jama’a a duniya, lura da yadda ake samun yaduwar cututtuka daga wannan yanki zuwa wancan a cikin iska.

A shekarar bara ma hukumar ta lafiya ta fitar da wani rahoto da ke cewa matsalar ta sauyin yanayi ta yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane milyan 7 a sassan duniya, sakamakon yadda jama’a ke shakar gurbataciyyar iska wadda a mafi yawan lokuta take dauke da cututtuka.

Hukumar ta bayar da misali da tsanantar zafi a wannan zamani wanda ya sa hatta a yankunan da ba a saba samun bullar cututtuka kamar zazzabin cizon sauro ba, a yau sun bayyana a can tare da kashe jama'a.

Misis Maria Neira, daya daga cikin manyan jami’ai a hukumar ta lafiya, ta ce domin ceto rayukan milyoyin mutane, ya zama wajibi ga mahalarta taron da za a fara a ranar 30 ga wannan wata na nuwamba a Faransa, su samar da yarjejeniya ta kasa da kasa a tsakaninsu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI