UNICEF

Rashin tsaftataccen makewayi matsala ce babba- UNICEF

Rashin tsaftace makewayi na haifar da matsaloli musamman ga kananan yara
Rashin tsaftace makewayi na haifar da matsaloli musamman ga kananan yara Getty Images/Flickr Open/Rudolf Vlcek

Rahoton da asusun kula da ilimin kananan yara na majalisar dinkin duniya ya fitar, wato UNICEF, na cewa karancin tsaftataccen makewayi matsala ce babba a kasashe masu tasowa kuma hakan na barazana ga lafiyar yara.

Talla

Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashen duniya biyar da ke fuskantar wannan matsalar a cewar rahoton.

Wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake bikin ranar makewayi ta duniya, inda asusun na UNICEF ya duba matsalolin da ake samu na rashin tsaftace makewayi da kuma alakar haka da tamowa ko karancin abinci mai gina jiki a tsakanin yara kanana.

Asusun ya ce, akalla al’ummar Najeriya miliyan hamsin na daga cikin mutane miliyan dari tara da arba’in da shida da ba su da tsaftacaccen makewayi, abinda ke sa wasu daga cikin al’ummar yin ba haya a bainal jama'a.

Rashin tsaftacaccen wurarren bahaya ya taka rawa a barkewar cutar amai da gudawa.

Asusun ya ce, dole a samo hanyar magance wadannan matsalolin na samar da wadatattun wuraren bahaya ga wannan al’umma, ganin kasa yin hakan ya zama gazawa a kokarin inganta rayuwar al’ummar kasashen da ke tasowa.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.