ISIS

IS ta jaddada cewa ita ta tarwatsa jirgin Rasha

Baraguzan jirgin fasinjan Rasha da IS ta yi ikirarin kakkabo wa
Baraguzan jirgin fasinjan Rasha da IS ta yi ikirarin kakkabo wa REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

Kungiyar mayakan IS ta sake jaddada cewar ita ta sanya bam din da ya tarwatsa jirgin fasinjan Rasha wanda ya hallaka mutane 224 bayan ta bai wa jami’an tsaron tashar jiragen Masar cin hanci. 

Talla

A wani labarin da ta wallafa a internet, kungiyar ta sanya hotan bam din wanda ke cikin gwangwanin lemo, da kuma hotan fasfo din da ta ce mayakanta sun samo na fasinjojin jirgin.

IS ta dade tana ikrarin kakkabo jirgin wanda binciken da Russia ta gudanar ya tababtar da haka.

A bangare guda shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Masar Abdel Fatah al- Sisi sun amince da wani shiri na kara matakan tsaro a jiragen samansu a matsayin matakin farko na mayar da harkar sufuri tsakanin kasashen biyu.

Kasashen biyu dai sun katse zirga zirgan jiragen sama a tsakaninsu bayan da jirgin na Rasha ya tarwatse a yankin Sinai na Masar.

Fadar Kremlin ta ce shugaban Putin ya shaida wa al-Sisi irin matakan da ya ke dauka kan kungiyar IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI