Faransa-MDD

Kudurin Majalisar Dinkin Duniya don murkushe ISIS

Zauren Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a New York
Zauren Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a New York REUTERS/Lucas Jackson

Kwamitinin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri da Faransa ta gabatar kan yadda za a kawo karshen ayyukan ta’addanci na kungiyar ISIS.

Talla

Wannan ne dai karo na farko da MDD ke jefa kuri’ar amincewa da wani kuduri da ya shafi kungiyar kai-tsaye, mako daya bayan hare-haren ta’addancin da a kai wa Faransa tare da kashe mutane 129.

Kudurin dai ya bayar da damar yin amfani da duk wata dama domin kai wa mayakan kungiyar hare-hare a cikin Syria da Iraki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.