Amurka-Faransa

Amurka da Faransa za su ci gaba da yakar ISIS

Shugaban Faransa Francois Hollande da takwaransa na Amurka Barack Obama.
Shugaban Faransa Francois Hollande da takwaransa na Amurka Barack Obama. 路透社

Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande da takwaransa na Amurka Barack Obama sun bayyana aniyarsu ta ci gaba da kai hari kan mayakan ISIS, inda suka bukaci Rasha ta bada hadin kai wajen warware rikicin kasar Syria da aka kwashe shekaru hudu ana yi.

Talla

Hollande ya bukaci goyan bayan Amurka wajen murkushe mayakan ISIS da kuma musayar bayanan sirri a tsakaninsu, amma ya ce babu wani shirin tura sojoji cikin kasar.

Shugaba Obama ya bayyana goyan bayansa ga al’ummar Faransa kan matakan da Faransa ke dauka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.