Rasha-Turkiya

Rasha ta yanke hulda da Turkiya

Rasha za ta yanke hulda da Turkiya saboda harbo jirginta da Turkiya ta yi tare da kashe mata matuki guda.
Rasha za ta yanke hulda da Turkiya saboda harbo jirginta da Turkiya ta yi tare da kashe mata matuki guda. 路透社照片

Ma’aikatar tsaron Rasha ta bayyana cewa kasar ta dakatar da huldar soji da Turkiya kuma ministan harkokin wajenta, Sergey Lavrov ya soke ziyar da ya shirya kai wa Turkiya sakamakon harbor jirgin yakinta akan iyakar Syria.

Talla

Kasar Turkiya dai ta harbor jirgin ne samfurin Sukhoi Su-24 bayan ta zargi Rasha da karya dokar keta sararin samaniyarta, lamarin ya bakanta ran shugaba Vladmir Putin na Rasha kuma ya bayyana abinda da Turkiya ta yi wa kasarsa a matsayin cin amana.

Har ila yau Rasha ta gargadi ‘yan kasarta da su dakatar da tafiye tafiye zuwa Turkiya, inda ta ce kasar ba wurin zama ba ne lura da matsalar tsaro.

Tuni dai Rasha ta aika jiragen yaki na ruwa zuwa kusa da gabar inda aka harbor jirgin, wanda ya fadi a kauyen Yamadi da ke Syria kuma daya daga cikin matuka jirgin ya rasa ransa.

A bangare guda, kungiyar tsaro ta NATO ta bukaci kasashen biyu da su kai zuciya nisa amma shugaban kungiyar Jens Stoltenberg ya ce suna goyon bayan Turkiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.