Amurka

Obama ya kwantar da hankulan Amurkawa

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Jonathan Ernst

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya nemi kwantar da hankulan Amurkawa da ke shirin bikin ranar Thanksgiving a yau, inda ya ce ba sa fuskantar wata barazanar harin ta’adanci.

Talla

Shugaban ya shaida wa Amurkawa cewa, gwamnati na daukar dukkan matakan da suka dace domin kare lafiyar al’ummar kasar, saboda haka dubban Amurkawan da suka shirya tafiye tafiye don gudanar da bukukuwan da za ayi a yau, na iya tafiyarsu ba tare da wata fargaba ba.

Obama ya ce, kawo yanzu babu wani bayanan sirri da ke nuna cewar ana shirin kai hari cikin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.