Amurka-IS

Wasu Sanatocin Amurka na son a tura dakaru don yakar IS a Syria

Senatan Amurka John McCain
Senatan Amurka John McCain Reuters

Wasu Sanatocin Amurka da suka hada da Sanata John McCain sun bukaci a tura sojojin kasashen duniya 100,000 cikin kasar Syria dominn kakkabe mayakan ISIL da ke da’awar jihadi a duniya.

Talla

McCain da Sanata Lindsey Graham da ke ziyara a Bagadaza babbar birnin kasar Iraqi sun soki manufofin gwamnatin Amurka na yaki da ISIS, inda suke cewa ya dace kasashen duniya su bada gudumawar sojojin da zasu shiga yaki da mayakan gadan-gadan..

A cewar Mista McCain ana bukatar rundunar Sojoji 100,000 daga manyan kasashen duniya.

‘Yan Majalisun sun kuma bukaci kara yawan sojojin Amurka a kasar Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI