Sida

Ranar yaki da cutar Sida ta duniya

Ana bikin yaki da Sida a 1 ga watan Disemba
Ana bikin yaki da Sida a 1 ga watan Disemba ONUSIDA

A yau 1 ga watan Disamba Majalisar Dinkin Duniya ta ware domi bikin yaki da cutar AIDS ko SIDA a duniya inda ake amfani da ranar don wayar da kan al’umma kan illolin cutar.

Talla

Sai dai akwai matsalolin da ake fuskanta a yaki da cutar da suka hada da rashin kulawa ko wadatar magani

Duk da kokarin kawar da cutar da kasashen duniya ke yi cutar Sida ta kasance babban kalubale ga masana kimiya musanman a kasashe masu tasowa.

Ana ci gaba da samun mutane da ke kamuwa da cutar inda ‘yan mata suke kasancewa cikin hatsarin kamuwa da fiye da sauran jama’a kamar yadda alkalumma suka nuna.

Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da amfani da wannan ranar na hada kan al’ummar duniya wajen yakar cutar tare da bai wa wadanda suka riga suka kamu da cutar goyon baya tare da nuna alhini ga wadanda suka rasa rayukans.u

Alkaluman hukumar lafiya ta Duniya na cewa mutane akalla miliyan 36 ke rayuwa da kwayar cutar ta Sida cikin su har da yara kanana akalla miliyan biyu da dari shida.

A shekara ta 2014 mutane miliyan 34 cutar ta kashe, yawancinsu a Nahiyar Afrika.

Kawo yanzu dai an gagara gano maganin da zai warkar da cutar baki daya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.