Faransa-MDD

Manyan kamfanonin kasashen duniya zasu fara amfani da makamashin wutar lantarki marar guba.

Turirin hayakin masana'antu dake gurbata yanayin duniya
Turirin hayakin masana'antu dake gurbata yanayin duniya Flickr/freefotouk

Shida daga cikin manyan kamfanonin kasashen duniya sun dauki niyar yin amfani da wutar lantarkin da kawai aka samar 100% daga makamashin da baya gurbata yanayi, bayan da a yau litanin suka bi sahun takwarorinsu sama da 50 da suka dauki wannan niya a zaman taron kasashen duniya na neman hanyoyin rage dumamar yanayi duniya da kashi 2 cikin 100%.

Talla

Kamfanonin Coca Cola, gungun BMW, International Flavors & Fragrances, Nordea Bank AB, Pearson PLC, da kuma Swiss sune kamfanonin baya bayan nan da suka bayyana aniyarsu ta bin sahun shirin gungun manyan kamfanonin kasashen duniya 53, da suka hada da Microsoft, Ikea da kuma Google mai taken +RE100+, na rage fitarda iska mai guba domin rage gurbata yanayin duniya, ta hanyar amfani da Tsanwan makamashin samar wutar lantarki da baya gurbata yanayin duniya

Hasashe dai ya nuna cewa wannan mataki da kamfanonin suka daukar na bukatar Karin samun sama da Terawateur 90 na wutarlantarki da ake samarwa ta tsanwar makamashi, da baya gurbata yanayi, wanda ke matsayin 1% na wutar lantarkin da kamfanoni ke sha a duniya, wanda kuma ita ce yawan wutar da biranen Hong Kong da Singapour kasha inji sanarwar tasanar ta yau litanin

Wannan mahawara ta samar da tsanwan makamashin dai zata bada damar yin tsimin rage fitar da kimanin ton miliyan 56 na hayaki mai guba na CO2 dake dumama duniya, inji Climate Group, kungiya da ke kokarin ganin kamfanonin na duniya sun kaura daga barin amfani da makamashin mai guba, zuwa tsanwan makamashin abokin tafiyar yanayi

Climate Group, tace idan har kamfanoni masu zaman kansu na amfani da tsanwan makamashin wajen samar da wutar lantarki gudanar da ayukansu zai bada damar rage kashi 15% na turirin iska mai guba dake kona shimfidar yanar sararin samaniya dake hana zafin rana keta sararin samaniya zuwa ga doron kasa, wanda hakan ke jawo ko wace irin illa ga duniya Ambaliyar ruwa Iska zai zaiyar kasa kwarara Hamada ko kuma tsananin sanyin hunturu da kuma cututuka wanda hakan ke haifar da babbar hasarar rayuka da tattalin arziki ga duniya.

Sanarwa ta kara da cewa, sai fa manyan kamfanonin duniya sun tashi tsaye, gaba daya, wajen kirkiro da kasuwannin samar da tsanwan makamashi mai girma, ne zai bada damar takaita ci gaban dumar yanayin da duniya ke fuskanta da kashi 2% kamar yadda Emily Farmworth, babbar darakta dake kula da yakin neman goyon bayan amincewa da sabuwar dubarar rage fitarda iskar mai guba ta RE100, ta sanar a yau litanin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.