Isa ga babban shafi
Amurka

An yi kokarin tatsar bayanan wasu a Twitter

Shafin Twitter
Shafin Twitter REUTERS/Dado Ruvic/Files
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 1

Kamfanin Twitter ya aika da sakon gargadi ga wasu masu amfani da shafin cewa gwamnati na kokarin tatsar bayanansu da suka hada da adireshin Imel da lambobinsu na salula.

Talla

Wannan ne karon farko da Twitter ya aika da irin wannan sakon na gargadi ga masu amfani da shafin.

Wasu da aka aika wa da gargadin sun wallafa sakon a shafinsu na Twitter.

Kuma a sakon Twitter ya ce ba a cim ma nasarar tatsar bayanan ba, amma yana gudanar da bincike akai.

Twitter ya taba yin gargadi cewa an tatsi bayanan mutane sama da 200,000 musamman a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.