Isa ga babban shafi
Colombia

Cutar Zika na barazana ga Masu juna-biyu

Cutar Zika barazana ce ga mata masu juna biyu.
Cutar Zika barazana ce ga mata masu juna biyu. REUTERS/Rodrigo Paiva
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau | Bashir Ibrahim Idris
Minti 1

Hukumomin Colombia sun ba mata shawara a kasar da su kaucewa daukar ciki sakamakon barkewar wata cuta da sauro ke yadawa da ake kira Zika.

Talla

Dubban mutane ne cutar ta shafa a watannin da suka gabata a kasashen Amurka da Latin.

Cutar ta shafi kasashe 14 a Yankin Latin Amurka, kuma ana kamuwa ta ita ne daga cizon sauro wanda ke shafar jinjirin dake ciki tare da sauya halittarsa.

An haifi dubban yara da ke dauke da wasu matsaloli a sassan jikinsu da aka danganta da cizon sauro.
Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace sauron da ke yada cutar Zika shi ne kuma ya ke sa cutar Zazzabin Maleriya.

Yanzu haka kuma rahotanni sun ce magani da gidan sauro ya yi tsada sakamakon bullar cutar Zika a Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.