Girka-Turkiya

'Yan gudun hijira 44 sun hallaka a tekun Girka

'Yan gudun hijira na ci gaba da tsallkawa Turai saboda matsaloli a kasashensu.
'Yan gudun hijira na ci gaba da tsallkawa Turai saboda matsaloli a kasashensu. REUTERS/Dimitris Michalakis
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 2

Dogaran gabar ruwar kasashen Girka da Turkiyya sun tabbatar da mutuwar bakin haure 44 cikin su har da kananan yara 20, sakamakon nitsewar kwale-kwalen da suke cike a teku a hanyarsu ta kutsa kai Girka, yayin da wasu da dama suka bace.

Talla

Duk da yanayi na hunturu da ake fama da shi a yanzu haka a Turai, dubun-dubatan wadanda ke barin kasashensu, saboda yaki na ci gaba da tsallaka tekun Mediterranean da nufin shiga Turai.

Kasashen Jamus da Turkiyya sun kasance wadanda suka taka rawar gani wajen tunkarar matsalolin kwararar bakin haure da ke addabar nahiyar Turai, kuma waziriyar Jamus Angela Merkel da ke karban bakwancin Firaministan Turkiya Ahmet Davutoglu a kasar a yanzu haka, ana saran su cimma matsaya kan wannan al’amari a ganawarsu

Sai dai tattaunawar ta su a yau Juma’a ba ga Merkel kawai ta ke da muhimmanci ba, wacce ke fuskantar kalubale da dama a kasarta kan tsugunar da bakin haure, suma kasashen Turai za ta amfane su, musamman kasashen da ke adawa da batun karban bakin haure.

A na ci gaba da samun rabuwan kawuna tsakanin kasashen Turai kan hanyar kawo karshan wannan matsalar ta bakin haure, yayin da Austria ke jaddada adadin bakin da za ta iya bai wa mafaka sabannin adadin da aka bukace ta da ta karba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.