Bakonmu a Yau

Dakta Tanko Zakari game da Cutar Zika

Sauti 03:09
Ana kamuwa da Cutar Zika ta hanyar Cizon Sauro
Ana kamuwa da Cutar Zika ta hanyar Cizon Sauro RFI
Da: Awwal Ahmad Janyau
Minti 4

Cutar zazzabin Zika da ake samu daga cizon Sauro na ci gaba da yaduwa daga yankin latin Amurka zuwa wasu kasashen Caribbean. An ruwaito bullar cutar a kasashe kusan 20 na Latin. Wasu kasashen da dama sun haramtawwa mata daukar Ciki har na tsaron shekaru biyu saboda cutar. Abdurrahman Gambo ya tattauna da Dakta Tanko Zakari, kwararren Likita a asibitin koyarwa na malam Aminu Kano da ke Najeriya.

Talla

An bayyana cewa Cutar zika ta samo asali ne daga Afrika kuma an samu bullarta ne a kasashen Latin Amurka a bara.

Ana kamuwa da cutar Zika ta hanyar cizon sauro kuma ta fi yin illa ga mata masu juna biyu, inda cutar sanadin haihuwar jariri da karamin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.