WHO-Zika

Cutar Zika na iya yaduwa a Afrika da Asiya

Sauro ne ke yada kwayar cutar Zika
Sauro ne ke yada kwayar cutar Zika Rafael Neddermeyer

Hukumar lafiya ta duniya ta gargadi cewa, cutar Zika za ta iya yaduwa zuwa yankunan Afrika da Asiya, inda aka fi yawan haihuwa a duk fadin duniya.

Talla

A ranar litinin ne hukumar ta WHO ta annaya dokar ta baci dangane da cutar ta Zika mai haddasa haihuwar jarirai da matsalar kwakwalwa ko kuma kananan kawuna yayin da ta shafi dubban jarirai a kasar Brazil.

Lura da darasin da aka koya daga cutar Ebola, yanzu haka hukumar lafiyar ta kafa wani sashen bayar da agajin gaggawa a Shalkwatanta da ya hada jami’ai daban daban na hukumar domin tinkarar wannan cutar ta Zika kamar yadda Anthony Costello, babban jami’in hukumar ya shaida wa manema labarai a jiya a birnin Geneva na kasar Switzerland.

A bangare guda, wani kamfanin harhada magunguna a kasar Faransa mai suna SANOFI ya sanar da fara gudanar da binciken hada maganin cutar ta Zika wadda sauro ke yada kwayarta kuma kamfanin ya bayar da tabbacin cewa za a samu mafita ga wannan annobar wadda har yanzu babu maganinta a duniya.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.