Isa ga babban shafi
Duniya

‘Yan Jaridu 2,297 sun gamu da ajalinsu cikin shekaru 25

Jaridun Argentina
Jaridun Argentina REUTERS/Ivan Alvarado
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
1 min

Akalla ‘yan jaridu 2,297 suka gamu da ajalinsu a fadin duniya, daga shekara ta 1990 zuwa yanzu, kamar dai yadda wata sanarwa daga cibiyar ‘Yan jaridu ta duniya ta sanar a Brussels.

Talla

Sanarwar na cewa cikin shekaru 25 da suka gabata rahotanni sun nuna cewa a kasar Iraqi aka fi kashe ‘yan jaridu

A cikin shekarar data gabata kawai ‘yan jaridu 112 suka rasa rayukansu a yake-yake da sauran tarzoma da suke tafiya domin dauko labarai.

Aikin Jaridar dai na fuskantar barazana a wannan lokaci da ayyukan ta'addanci ke sake tsananta a wasu yankunan duniya, musamman gabas ta tsakiya da wasu yankuna Afrika har ma da Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.