CANADA

Canada za ta bai wa Amurkawa mafaka saboda Trump

Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican na samun nasara a yakin neman zabensa
Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican na samun nasara a yakin neman zabensa REUTERS/Tami Chappell

Wani tsibiri mallakin kasar Canada ya ce zai karbi Amurkawan da ke adawa da salon siyasar Donald Trump mai nuna adawa a fili da shigar baki a kasar.

Talla

Tsibirin Cap-Breton, wanda ke da tazarar kilomita 400 daga Amurka, ya ce idan har Trump ya yi nasara a zaben kasar da za a yi, to zai karbi wadanda ba sa son zama a Amurka domin ci gaba da rayuwarsu a tsibirin mallakin Canada.

Wata sanawar da tsibirin ya fitar a shafin intanet ta bukaci masu bukatar neman mafakar siyasa da su gaggauta zuwa gabanin ma Donald Trump ya lashe zaben.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.