WHO-Zika

Zika na haifar da shanyewar jiki

Cizon Sauro ke yada Cutar Zika
Cizon Sauro ke yada Cutar Zika REUTERS/Ivan Alvarado

Masu bincike a Faransa sun gano cewa kwayar cutar zika ba mata masu juna biyu kawai take yi wa illa ba, Cutar kan haifar da shanyewar jiki.

Talla

A cewar Annie Lannuzel ta asibitin Pointe–a-pitre da ke tsibirin Guadeloupe a yankin Caribbean, bayan aiwatar da gwaje-gwajen kan wata yarinya mai shekaru 15 da jikinta ya shanye, an gano cewa tana dauke ne da kwayoyin cutar Zika.

Wannan shi ne karon farko da ake danganta shanyewar jiki da cutar da ke yaduwa a yankunan kasashen kudancin Amurka.

Masana kimiya a makon sun rawaito cewa bayan dogon nazari da bincike sun gano sabbin illolin da kwayar da cutar Zika ke haifarwa baya ga haihuwar jarirai da karamin kai.

Bincike ya kuma bayyana cewa Zika na nakasu ga garkuwar jiki kuma ba mai ciki kawai ta ke wa illa ba.

Har yanzu dai babu wani cikakaken rigakafin cutar.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace cutar a yanzu ta yadu zuwa kasashe 41, sai dai ta fi illa a Brazil inda mutane miliyan guda da rabi suke dauke da ita, yayin da aka haifi jarirai 641 da nakasa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.