Amurka

Rubio ya caccaki Trump akan musulunci

Sanata  Marco Rubio da Donald Trump.
Sanata Marco Rubio da Donald Trump. REUTERS/Carlo Allegri

Mai neman tsayawa takarar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar Republican, sanata Marco Rubio ya caccaki abokin hamayyarsa Donald Trump kan kalaman da ya furta game da addinin Islama.

Talla

Mr. Trump ya ce addinin Islama na kyamar kasar Amurka, abinda ya sa Mr.Rubio ya caccake sa a muhawarar da suka tafka a birnin Miami na jihar Florida, a ci gaba da fafutukarsu ta neman wakiltan jam'iyyar Republican a zaben shugaban kasar Amurka mai zuwa.

To sai dai Mr.Rubio ya ce, musulunci na fama da masu ra’ayin rikau amma duk da haka akwai musulman Amnurka da dama da ke alfahari da kasancewarsu ‘yan kasar ta Amurka.

Rubio ya kara da cewa, bai dace shugabanni su rika furta kalamai ta yadda suka ga dama ba saboda akwai abinda ka iya biyo baya.

A hirar da ya yi da wata kafar talabijin Mr. Trump dai ya ce, mabiya addinin Islama na nuna mu su kiyayya.

Sanata Rubio da sauran abokan hamayyarsa, sanata Ted Cruz da Gwamnan Ohio John Kasich duk sun bayyana cewa., Amurka na bukatar ci gaba da hulda da kasashen musulmai da ke yankin gabas ta tsakiya domin za su taimaka wajen yaki da kungiyar ISIS mai da’awar jihadi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.