Brazil

'Yan Kasar Brazil Na shirin bore Mai muni.

A kasar Brazil mutane sama da miliyan daya ake ganin za su shiga zanga-zanga a yau lahadi domin nuna kyamar Gwamnati da neman shugaban kasar Dilma Rousseff ta sauka.  

Shugaban Brazil  Dilma Rousseff
Shugaban Brazil Dilma Rousseff PHOTO/ KENA BETANCUR AFP
Talla

Wannan bore na zuwa ne a wani lokaci da Birnin Rio de Janeiro dake kasar ke sa rai zai karbi bakuncin gasan wasannin Olympics a watan Augusta, gashi matsalolin komadan tattalin arziki da rikicin siyasa ya dabaibaye kasar.

Shugaba Dilma Rousseff ta yi ta roko ga alummar kasar da su kiyaye a guji shiga bore mai muni.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI