UNICEF

Miliyoyin mutane na shan gurbataccen ruwa- UNICEF

UNICEF ta ce, kusan mutane miliyan 663 ke shan gurbataccen ruwa a duniya
UNICEF ta ce, kusan mutane miliyan 663 ke shan gurbataccen ruwa a duniya REUTERS/Juan Carlos Ulate

Hukumar UNICEF ta ce, kokarin samarwa miliyoyin mutane tsabtacaccen ruwan sha na ci gaba da zama babban kalubale sakamakon sauyin yanayi da kuma rashin tsabta a cikin al’umma. 

Talla

A cikin sanarwar da hukumar ta bayar kan bikin ranar samar da ruwa ta duniya da a keyi a yau, UNICEF ta ce, yayin da aka kawo karshen muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya a bara, har yanzu akwai mutane miliyan 663 a duniya da basa samun tsabtacaccen ruwan sha, yayin da biliyan daya da miliyan 800 ke shan gurbataccen ruwa.

Sanarwar ta kuma ce, yanzu haka mutane kusan biliyan biyu da rabi ne ba su da ban-daki a duniya, yayin da biliyan daya kuma, ke bayan gida a filin Allah, matsalar da ke haifar da cututtuka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.