Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta taya Syria murnar kwace Palmyra

Shugban Syria Bashar al-Assad da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin
Shugban Syria Bashar al-Assad da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin REUTERS/Alexei Druzhinin/RIA Novosti/Kremlin
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Bashir Ibrahim Idris
Minti 2

Fadar shugaban kasar Rusha ta ce shugaba Vladimir Putin ya taya takwaransa na Syria Bashar al- Assad murnar nasarar da dakarunsa suka samu ta kwace garin Palmyra daga hannun mayakan ISIS.

Talla

Mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce, shugaba Putin ya kira Assad ta wayar tarho inda ya yaba da rawar da sojojin kasar suka taka na sake kwace garin daga mayakan ISIS.

Jami’in ya jiyo Putin na cewa, duk da yake ya janye wani sashe na sojojin kasar daga Syria, sojojin Rasha za su ci gaba da taimaka wa na Syria domin yaki da 'yan ta’adda a kasar don ganin sun raba kasar da masu tayar da kayar baya.

Shi kuma a na shi kalaman, shugaba Bashar al- Assad ya yaba da goyan bayan da sojojin saman Rasha ke bai wa kasarsa, inda yake cewa, babu  yadda za su samu nasarar kwace gari irin Palmyra ba da taimakon Rasha ba.

Shugaba Putin ya yi kuma magana da shugabar hukumar bunkasa ilimi da kimiya da kuma raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, inda ya shaida ma ta cewa, Rasha za ta yi aiki da sojojin Syria wajen kawar da bama-baman da aka binne a Palmyra mai matukar tarihi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.