Isa ga babban shafi
Girka

Girka ta fara mayar da bakin haure

An fara mayar da bakin haure daga Girka zuwa Turkiya
An fara mayar da bakin haure daga Girka zuwa Turkiya Reuters
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Hukumomin Girka sun fara mayar da gungun ‘yan gudun hijira zuwa kasar Turkiya a karkashin wata yarjejeniya mai cike da rudani wadda da aka cimma domin magance matsalar kwararar bakin haure a Turai.

Talla

Rahotanni sun ce, jirajen ruwa guda uku sun kwashe bakin haure kimanin 200 daga tsibirran Lesbos da Chios na Girka, inda aka kai su Turkiya.

Akasarain bakin da aka kwashe a yau Litinin, ‘yan asalin kasashen Pakistan da Bangladesh ne yayin da hukumar kula da shige da fice ta Girka ta ce, bakin ba su nemi izinin fakewa a kasar ba.

Hukumar da ke kula da kan iyakokin Turai ta ce, ana aikin kwashe bakin cikin tsanaki kuma an jibge jami’an kwantar da tarzoma da kuma ‘yan sanda.

A bangare guda, suma hukumomin Jamus sun bayyana cewa, tawagar farko ta ‘yan gudun hijirar Syria da ke neman mafaka sun isa kasar daga birnin Santanbul kuma a wanann yammacin ne tawaga ta biyu za ta isa Hanover na Jamus din duk dai a karkashin wannan yarjejeniya wadda ta ce Turai za ta karbi dan gudun hijirar Syria guda a madadin wanda Turkiya ta karba daga Girka.

Shugabannin tarayyar Turai na fatan wannan yarjejeniya da suka kulla da Turkiya za ta taka rawar gani wajen hana bakin hauren yin tattaki domin shiga Turai, abinda ya yi sanadin mutuwar da dama daga cikin su.

To sai dai kungiyoyin kare hakkin dan adam sun caccaki wannan mataki na musayar bakin, yayin da Amnesty International ta ce, Turkiya ba tudun mun tsira ba ne ga bakin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.