Jamus

'Yan sanda sun kai samame kan masu kutse na duniya

Jami’an ‘Yan sanda sun kai samame a kasashen Jamus da Netherlands da Faransa da Canada akan masu kutse a shafukan intanet inda suka yi nasarar cafke babban wanda ake zargi.

'Yan sanda sun kai sameme kan kwararrun masu kutse a kasashen Faransa da Jamus da Netherlands da Canada
'Yan sanda sun kai sameme kan kwararrun masu kutse a kasashen Faransa da Jamus da Netherlands da Canada
Talla

‘Yan sandan sun kai wannan samame ne da nufin kama mutane 170 da ke aikata laifi ta hanyar amfani da intanet kuma sun samu nasarar cafke wani matashi mai shekaru 22 wanda hukumomin jamus suka ce shi ne wandan aka fi zargi.

Kimanin ‘yan sanda 700 suka kaddamar da samamen a gidaje daban daban da wuraren gudanar da harkokin kasuwanci yayin da suka samu makamai da miyagun kwayoyi bayan sun kama wanda aka fi zargin.

Rahotanni sun ce, su dai wadanann kwararrun ‘yan kutsen na amfani da wata manhaja ce domin su saci lambobin sirri da kuma bayanan sirri na bankuna, abinda ke saukake msusu yin kutse har su sace kudaden jama’a.

A cikin wata sanarwa da suka fitar, jami’an ‘yan sandan sun ce, sun kwace kamfutoci guda 300 da suka hada da faya- fayai mallakan masu kutsen.

Masu shigar da kara na Jamus sun ce, wannan samame da ‘yan sanda 700 suka kaddamar a cikin tsari a wadannan kasashe, an kai shi ne kan jiga- jigan masu kutse na duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI