Bakin haure

Bakin haure 15 sun bace a teku

Ana ci gaba da samun asarar rayukan bakin haure da ke kokarin tsallakawa Turai
Ana ci gaba da samun asarar rayukan bakin haure da ke kokarin tsallakawa Turai REUTERS

Majalisar dinkin duniy ta ce, wasu baki 15 sun bace bayan da kwale kwalen da suke ciki ya nitse a tekun Mediterranean.

Talla

Mai magana da yawun hukumar kula da 'yan gudun hijira Carltta Sami, ta ce kwale kwalen ya yi hadari ne lokacin da yake dauke da baki kusan 120, kuma akasarin su 'yan Afrika ne.

Labarin na zuwa ne bayan da kungiyar da ke sa ido kan masu kaura ta sanar da bacewar baki 84.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI