Girka

Girka ta fara kwashe baki daga sansanin Idomeni

Girka na kwashe 'yan gudun hijirar daga sansanin Idomeni da ke kan iyakar kasar da Macedonia
Girka na kwashe 'yan gudun hijirar daga sansanin Idomeni da ke kan iyakar kasar da Macedonia AFP

Hukumomin Girka sun fara kwashe dubban ‘yan gudun hijira da ke cikin wani hali daga sansanin Idomeni da ke kan iyakar kasar da Macedonia. 

Talla

An dai fara aikin kwashe su ne da asubahin yau Talata, inda aka tanadi motoci da ke jigilar su zuwa wasu sansanonin da hukumomin kasar suka ce, sun fiye wa ‘yan gudun hijirar alheri, amma 'yan gudun hijirar na tunanin kawai dabara ce ta kara nisanta su daga iyakar Macedonia da suke neman kutsawa.

An dai jibge jami’an kwantar da tarzoma baya ga tabbacin da hukumomin suka bayar na cewa, ba za a yi amfani da karfi wajen kwashe bakin ba.

A cikin watan Fabarairun daya gabata ne, sansanin ya cika makil bayan Macedonia ta rufe kan iyakarta, abinda ya jefa fiye da ‘yan gudun hijira dubu 8 cikin mawuyacin hali.

Akasarin ‘yan gudun hijirar dai, sun fito ne daga kasashen Syria da Iraqi da Afghanistan da ke fama da yake yake.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.