Japan-G7

G7 na taron tatttalin arziki a Japan

Kasashen G7 masu arzikin masana'antu a duniya
Kasashen G7 masu arzikin masana'antu a duniya Mandatory credit Kyodo/via REUTERS

Shugabannin manyan kasashen duniya masu arzikin masana’antu na gungun G7 sun fara sun fara tattaunawa a kasar Japan a yau, kafin gobe alhamis su fara gudanar da babban taronsu da zai mayar da hankali kan matsalolin tattalin azikin duniya da yaki da 'yan ta’adda da kuma matsalar kwararar bakin haure.

Talla

Shugabannin kasashen Japan da Amruka da France da Jamus da Birtaniya da Italiya  da kuma Canada ne  suka fara isa  karamin garin Ise-Shima mai gabar ruwa da ke tsakkiyar Japan a maraicen yau.

Rahotanni sun bayyana daukar tsauraran matakan tsaro da ba a taba ganin irin sa ba a kasar ta Japan a kan hanyoyin jiragen kasa da mota da na ruwa a yankin da za a gudanar da taron.

Shugaban Amurka Barack Obama ya isa  yankin zaman taron na G7, kafin ya ziyarci birnin Hiroshima bayan kammala taron, inda zai kasance shugaban Amruka na farko da zai tsoma kafa a birnin da Amurka ta jefa wa makamin nukliya a lokacin yakin duniya na shekarar 1945.

Shugaba Obama zai tattauna a fannin diflolmasiya da mai masaukinsa Firaministan Japan Shinzo Abe, zai kuma gana da David Cameron na Birtaniya wanda kasarsa ta haifar da shakku ga kungiyar ta G7 dangane da matakin kiran zaben raba gardamar al'ummar kasar Birtaniya a ranar 23 ga watan  gobe na ficewarta daga kungiyar tarayyar Turai ko kuma a a.

Shugaban  Fransa François Hollande da waziriyar Jamus Angela Merkel a gobe alhamis da safe ne za su isa a kasar, 'yan kwanaki bayan ministocin kudin kasashen 7 sun gudanar da zaman taronsu kan koma bayan tattalin arzikin da duniya ke fuskanta, wanda kuma shi ne babban maudu’in da zai mamaye taron na G7 masu karfin arzikin masana’antu na duniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.