Amurka

Trump ya samu adadin wakilai na tsayawa takarar

Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican na samun nasara a yakin neman zabensa
Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican na samun nasara a yakin neman zabensa REUTERS/Jonathan Ernst

Donald Trump wanda ke neman jam’iyyar Republican ta tsayar da shi takarar neman shugabancin Amurka a zabe mai zuwa, ya samu adadin mutanen da ake bukata domin su kaddamar da shi a matsayin dan takarar.

Talla

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press, ta ce Trump na da goyon bayan masu jefa kuri’a 1,238, sama da adadin da ake bukata kafin kaddamar da dan takara a jam’iyyar ta Republican.

Trump ya yi nasaran kawar da 'yan takara 16 da suka fito daga wannan Jam'iyyar tun a farkon tafiyar, inda daga karshe mutane biyu da suka rage a fafatawar suka janye bayan rashin nasara a zaben fidda gwani da aka gudanar a jihohin kasar na Amurka.

Sai dai Jam'iyyar Republican ba ta bayanna Donald Trump a matsayin dan takaranta a hukumance ba, har sai ta gudanar da taron ta na kasa a watan Yuli mai zuwa, inda 'ya'yan Jam'iyyar zasu tabbatar da wadanda suke naam da shi.

A baya dai Jigajigan Jam'iyyar Republican sun nuna adawarsu da takarar Trump da suka ce, Manufofinsa sun saba da na Jam'iyyar.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama na cigaba da sokar takarar Trump da ya ke cewa bashi da inganci zama shugaba a Amurka.

Amma ga dukkan alamu Trump ne zai fafata da Hillary Clinton na Democrat a zaben Shugabanci Amurka watan Nuwamba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI