Saudiya

Za a fara azumin ramadan gobe litinin

Wani dan kasar Saudiya ya kasa Dabino a kasuwa kafin soma Azumin watan Ramadan a yankin Utaiqah da ke kudu da birnin Riyath.
Wani dan kasar Saudiya ya kasa Dabino a kasuwa kafin soma Azumin watan Ramadan a yankin Utaiqah da ke kudu da birnin Riyath. REUTERS/Faisal Al Nasser

Kasashen Saudiyya da Qatar da Daular Larabawa da kuma Yemen sun sanar da ganin watan Ramadan abinda ke nuna fara azumi a gobe litinin.

Talla

Kasashen hudu sun sanar da ganin jinjirin watan ne yau lahadi wanda zai baiwa al’ummar Musulmi damar gudanar da daya daga cikin ibadar da aka umurce su na kauracewa cin abinci, shan ruwa da kuma jima’I daga fitowar rana zuwa faduwar sa.

Watan Ramadana na da matukar muhimmanci ga al’ummar Musulmi saboda falalar dake cikin sa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.