Bakonmu a Yau

Mustapha Marafa kan taron yaki da cutar Sida na MDD a Turai

Sauti 03:21
BERTRAND GUAY / AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta soma taron yaki da cutar Sida ko HIV/Aids a yau Laraba inda hukumomi daga sassan kasashen duniya zasu yi muhawara a kan yadda za a magance matsalar wariyar da masu dauke da cutar ke fuskanta da kuma yadda za a yaki cutar daga nan zuwa shekarar 2030.

Talla

Sai dai an haramtawa kungiyoyin kare hakkin ‘yan luwadi da madigo shiga zauren taron kamar yadda kasashen Rasha da Kamaru da Tanzania da kuma kungiyoyin kasashen musulmi suka bukata.

Awwal Janyau ya tattauna da Mustapha Marafa babban jami’in gudanarwar hukumar yaki da cutar Sida a jihar Zamfara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.