MDD

Adadin yara da ke tsallakawa zuwa Turai ya karu

Masu kokarin tsallaka teku zuwa Turai na yawan rasa rayukansu
Masu kokarin tsallaka teku zuwa Turai na yawan rasa rayukansu REUTERS/Marina Militare

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya ya ce, adadin yaran da suka tsallaka tekun Mediterranean zuwa Turai ba tare a iyayensu ba ya rubanyya har sau biyu a cikin watanni biyar na farkon wannan shekara.

Talla

Asusun na UNICEF ya ce, wani abin damuwa a game da wannan matsalar shi ne yadda yara 9 daga cikin 10 da suka shiga Turai, sun shiga nahiyar ne ba tare da iyaye ko kuma wani makusancinsu ba.

A wani rahoto da ta fitar UNICEF ta ce, yanzu haka akwai yara sama da dubu 7 da suka shiga Turai daga Afrika a cikin watanni 5 na wannan shekara, kuma hakan na a matsayin babban hatsari ga makomarsu nan gaba.

Rahoton asusun na majalisar dinkin duniya na nuni da cewa, da dama daga cikin yaran ba sa tare da iyayensu ne tun a gida, yayin da wasu suka rasa rayukansu ta hanyar nutsewa a teku lokacin da suke kokarin shiga Turai.

Ita ma hukumar kula da bakin Haure a duniya IOM ta ce, adadin mata da kuma ‘yan mata ‘yan asalin Najeriya da ke zaune a Libya kan hanyarsu ta zuwa Turai, ya kai wani matsayi da ke tayar da hankula.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.