Egypt- Saudi

Kotu a Masar ta Soke Kyautar da aka yi da wani tsubiri a Maliya ga Kasar Saudiya.

Shugaban Masar  Abdel Fattah al-Sisi  ta hagu tare da Sarki Salman na Saudiyya a lokacin da Sarkin ya sauka a birnin Cairo.
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ta hagu tare da Sarki Salman na Saudiyya a lokacin da Sarkin ya sauka a birnin Cairo. REUTERS/The Egyptian Presidency/Handout via Reuters

Wata Kotu a kasar Masar ta soke wani matakin da Gwamnatin kasar ta dauka na yin kyauta da wani Tsubiri a tekun Maliya ga Kasar Saudiya.

Talla

Tsubirin na cikin tekun Maliya ne da ya raba kasar Masar da Saudiya.

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya sanar da kyautar da tsubirin cikin watan Afrilu a lokacin da Sarki Salman na Saudiya ya ziyarci Masar.

Wani Alkali ya shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP cewa Babbar kotun kasar ta rusa wancan kyauta da Gwamnati ta yi da tsubirin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.