Syria-Jordan

An katse bai wa 'yan hijirar Syria agaji a Jordan

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Syria
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Syria Reuters/路透社

Dubban ‘yan gudun hijirar Syria na cikin halin kunci a kan iyakar kasar da Jordan, bayan gwamnatin Amman ta hana su samun mafaka a sansanin Rukban saboda harin da mayakan jihadi suka kai kan iyakar a makon jiya. 

Talla

Kimanin ‘yan gudun hijirar Syria dubu 70 ne ke cikin halin kunci, inda suke fuskantar tsananin zafi da rashin isasshen abinci da ruwan sha, amma duk da wannan halin gwamnatin Jordan ta hana su shiga cikin kasarta saboda harin makon jiya da ya lakuma rayuka.

‘Yan gudun hijirar sun shafe tsawon watanni suna samun agajin abinci da ruwan sha daga kungiyoyin agaji daban daban na duniya amma tun lokacin da aka kaddamar da harin suka katse bayar da agajin.

Mai magana da yawun hukumar samar da abincin agaji ta majalisar dinkin duniya a Jordan, Shaza Moghraby ta ce, an dakatar da duk wani taimako da ‘yan gudun hijirar ke bukata.

Hukumomin Jordan sun ce, sansanin Rukban ya zama matattarar mayakan jihadi, abinda ya sa suka tsaurara tsaro don gudun bai wa ‘yan ta’adda mafaka a kasar.

Iyakar Rukban dai, ita ce babbar hanyar da ‘yan hijrar Syria ke bi domin shga Jordan kuma tun lokacin da rikicin Syria ya tsananta a bara , adadin masu hijrar Syria da ke neman mafaka a Jordan ya karu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.