Saliyo

Wani mutun ya kusan kona jirgin Faransa a Saliyo

Jirgin kamfanin Air France na Faransa
Jirgin kamfanin Air France na Faransa Steven Sunshine/airfrance.com

Hukumomin Saliyo sun gurfanar da wani dan kasar da ake zargi da yunkurin sanya wuta a jirgin sama na Air France bayan ya kutsa kai cikin tashar jirgin da ke Freetown ba tare da fasfo ko takardar shiga jirgin ba.

Talla

Hukumomin da ke kula da filin jirgin sun yi alkawarin tsaurara matakan tsaro bayan Ibrahim Kanu ya yi kokarin shiga cikin jrigin na Faransa dauke da man feitr da ashana da kuma tabar sigari a hannunsa.

Har ila yau an zargi Kanu da shiga kilattacen wurin da ma'aikata kadai ne ke shiga, inda ya da dauki motar da jirgin ke amfani da ita.

Jirgin dai mai lamba Airbus 330-220 na shirin zuwa birnin Paris ne na Faransa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.