Kotun ICC ta Kara Amincewa Da Hukuncin Daurin Shekaru 22 ga Shugabannin Serbia
Wallafawa ranar:
Alkalan kotun kasa-da-kasa dake hukunta masu aikata laifukan yaki, ICC a takaice sun yi watsi da daukaka kara na wasu tsoffin shugabannin Serbia biyu dake jayayya da hukuncin dauri na tsawon shekaru 22 saboda aikata laifukan kisan kiyashi.
Jagororin Serbiyawan Mico Stanistic da Stojan Zupijanin sun daukaka kara ne suna ja da hukuncin da aka zartas a shekara ta 2013 inda aka samu suna da hannu tsundum wajen kashe Musulmi a Bosnia, da Croatia da sauran wadanda ba Serbiyawa ba, tsakanin shekara ta 1992 zuwa shekara ta 1995.
Mutanen biyu sun kasance na hannun daman shugaba Radovan Karadzic wanda aka same shi da hannu cikin watan 3 na wannan shekara, da laifin kisan kiyashi na mutane dubu 100, da sa mutane miliyan 2 da dubu dari biyu su rasa muhalli.
Bangaren daukaka kara na kotun ICC sun yi watsi da bukatar mutanen, inda kotun ke nanata hukuncin farko na zama gidan maza na tsawon shekaru 22.
Masu shigar da kara na ganin hukuncin anyi sassauci, ganin irin rayukan mutane da suka salwantar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu