Iraqi

IS ta kashe mutane 125 a Bagadaza

Cincirindon mutane a wurin da aka kaddamar da harin na Bagadaza
Cincirindon mutane a wurin da aka kaddamar da harin na Bagadaza Reuters/路透社

Akalla mutane 125 ne suka rasa rayukansu yayin da 150 suka jikkata sakamakon wani kazamin harin kunar bakin wake da kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamarwa a birnin Bagadaza na kasar Iraqi.

Talla

Jami’an ‘yan sanda sun ce, wata mota ce makare da bama-bamai ta tarwatse a wata unguwa mai cike da hada-hadar jama’a a yankin Karrada na Bagadaza.

Rahotanni sun ce, an kai harin ne a dai dai lokacin da jama’a ke kan ganiyar gudanar da harkokin kasuwanci saboda azumin Ramadan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI