Aids

Masana sun shiga binciken gano maganin Sida

Kwayar Truvada da masu cutar Sida ke sha
Kwayar Truvada da masu cutar Sida ke sha AFP/Kerry Sheridan

Masana kimiya sama da 50 sun kaddamar da wani shirin shiga aikin binciken maganin da zai kawo karshen cutar Sida a duniya da ake kira Kabari Salamu Alaikum.

Talla

Cutar Sida ta kasance babbar kalubale ga masana kimiya wajen kokarin ganin an shawo kan cutar da ke kisan jama’a.

Akan haka ne masana kimiya sama da 50 suka kaddamar da shirin shiga aikin bincike domin samun maganin cutar karkashin jagorancin Barre-Sinoussi mai lambar yabo ta Nobel a bangaren likitanci.

An dai shafe shekaru ana neman maganin cutar Sida da wasu ke kira Kabari Salamu alaikum.

Sinoussi ta ce binciken yanzu ya kasance babban muhimmin abu da suka sa gaba tare da bayyana fatar samun nasara saboda kwarin guiwa daga masanan da za su shiga aikin binciken, wanda ya nuna za a iya samun maganin cutar.

Binciken Masaniyar kimiyar ce dai ya gano kwayar cutar da ke kawo cutar Sida a 1983.

Masanan za su gana a wani babban taron da za su gudanar na kwanaki hudu a Durban kasar Afrika ta kudu kan cutar Sida daga ranar 18 ga wata zuwa 22 ga watan nan na Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI