Amurka

Obama ya bukaci Amurkawa su hada kansu

Shugaba Obama tare da matarsa da kuma George W. Bush da Mike Rawlings a lokacin nuna juyayin kisan Dallas
Shugaba Obama tare da matarsa da kuma George W. Bush da Mike Rawlings a lokacin nuna juyayin kisan Dallas REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Amurka Barack Obama ya bukaci al’ummar kasar da su hada kansu wajen kawar da bambancin da ke tsakaninsu don ganin kasar ta samu ci gaba.

Talla

Yayin da ya ke jawabi a wajen taron juyayin kashe wasu jami’an 'yan sanda 5 a Dallas wanda ya samu halartar tsohon shugaban kasar George Bush da mataimakin shuagban kasa Joe Biden, Obama ya gabatar da jawabi mai sosa zuciya kan irin rawar da jami’an 'yan sandan ke bayarwa don kare lafiyar Amurkawa.

Obama ya ce, a matsayinsu na 'yan Adam su kan yi kuskure amma kuma bai dace ayi amfani da haka wajen raba kan al’ummar kasar ba.

Shugaban ya sake amfani da damar wajen sake kira don takaita mallakar bindiga a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.