Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa na gwajin kai hari a sansanin sojin Amurka

Gwajin Makami mai linzami da koriya ta arewa ke aiwatar wa
Gwajin Makami mai linzami da koriya ta arewa ke aiwatar wa KCNA/via REUTERS/File Photo.

Kasar Koriya ta Arewa tace harba makaman ‘Ballistic missilles’ da tayi wani gwaji ne kan yadda zata harba makaman nukiliya kan sansanin sojin Amurka dake kasar Koriya ta Kudu, kuma shugaban kasar Kim Jong Un da kan sa ya sa ido lokacin da aka yi gwajin.

Talla

Kamfanin dillancin labaran kasar yace shugaba Kim ya bada umurnin yin gwajin kan yadda za’a kai hari kan tashoshin jiragen ruwan Koriya ta kudu da filayen jiragen sama da sojojin Amurka suka yi sansani.

Sojojin Koriya ta kudu sun ce makaman sun ci zangon da ya kai kilomita 500 zuwa 600.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.