Birtaniya

Ana nazari kan makomar Birtaniya a MDD

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya  Ban-Ki-moon tare da shugaban kasar Suadan ta Kudu a birnin Juba
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban-Ki-moon tare da shugaban kasar Suadan ta Kudu a birnin Juba REUTERS/Jok Solomon

Wasu Jami’an Majalisar Dinkin Duniya na tambayoyi kan ko ya dace Birtaniya ta ci gaba da rike kujerar din-din-din a kwamitin na majalisar sulhu bayan ta janye 'yan sandanta da ke aikin samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu a lokacin da akayi rikicin makon jiya ba tare da tuntubar majalisar ba.

Talla

Wani rahotan sirri ya bayyana cewar, su ma kasashen Jamus da Sweden sun janye 'yan sandansu daga kasar ba tare da sanar da kowa ba kuma Majalisar ta haramta wa dukkanin kasashen uku maye gurbin jami'an 'yan sandan da wasu  idan yanayin tsaro ya inganta a Sudan ta Kudu.

Rahotan wanda jami’ai suka gabatar wa Sakatare Janar Ban Ki Moon ya ce, matakin janye 'yan sandan ya haifar da gagarumar matsala wajen gudanar da aikin samar da tsaro tare da rage lagwan jami'an tsaron da ke aiki a kasar ta Sudan ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI