Afrika

An kammala taron kasashen duniya kan HIV

Sama da mutane miliyan 30 suka rasa rayukansu cikin shekaru 35 saboda cutar HIV ko kuma kanjamau
Sama da mutane miliyan 30 suka rasa rayukansu cikin shekaru 35 saboda cutar HIV ko kuma kanjamau DR

An kammala taron kasashen duniya kan cutar Sida a kasar Afrika ta kudu, inda mahalarta taron suka bukaci karin bada tallafi don gudanar da binciken samun maganin cutar wadda yanzu haka ta kama mutane miliyan biyu da rabi a duniya.

Talla

Shugabar kungiyar masu yaki da cutar mai jiran gado, Linda-Gail Bekker ta ce har yanzu ba a samu nasarar magance cutar ba, duk da kokarin da kasashen duniya ke yi, ganin yadda mutane 15,000 masu fama da cutar suka mutu a cikin kwanaki 5 da aka kwashe ana taron, kuma 1,500 daga cikin su yara kanana ne.

Masana kimiya 15,000 suka halarci taron a Durban don nazari kan cutar da ta hallaka mutane sama da miliyan 30 a cikin shekaru 35 da suka wuce.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI