Rasha

Rasha ta samu sassauci a Wasannin Olympics

Shugaban Kwamitin Wasannin Olympic Thomas Bach
Shugaban Kwamitin Wasannin Olympic Thomas Bach REUTERS/Denis Balibouse

Kwamitin wasannin Olympic ya sassutawa ‘Yan wasan Rasha daga haramtawa dukkanin ‘yan wasan kasar shiga wasannin da za a gudanar a Rio na Brazil, sakamakon zargin da ake wa ‘Yan wasan na Rasha da shan abubuwa domin karin kuzari.

Talla

Yanzu kwamitin na wasannin Olympics ya mika hukuncin ne ga hukumomin wasannin kasashen da zasu fafata a wasannin domin su tantance ko ‘Yan wasan na Rasha na da damar shiga wasannin na Rio da za a soma a ranar 5 ga Agusta.

Shugaban kwamitin wasannin ya ce sun dauki matakin ne domin kare ‘yancin wasu daga cikin ‘yan wasan na Rasha da ba su da laifin shan kwayu.
Amma akwai matakai da kwamitin ya shata kafin ba dan wasan Rasha damar shiga wasannin na Olympic a Brazil

Duk wani dan wasa da aka taba dakatarwa saboda laifin shan abubuwa masu sa karin kuzari ba zai shiga wasannin na Rio ba

Wannan matakin na zuwa ne bayan rahoton da aka bankado da ya zargi kasar rasha akan ta dade tana goyon bayan wasu daga cikin yan wasaninta da ke shan abubuwa domin samun karin kuzari.

Tuni dai Rasha ta yi na’am da matakin, wanda ta danganta a matsayin ci gaba ga wasannin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.