Amuruka

Zan binciki Faransawa kafin su shiga Amurka-Trump

Trump ya lashi takobin binciken Faransawa
Trump ya lashi takobin binciken Faransawa

Donald Trump da ke takarar Shugabancin Amurka a jam’iyyar Republican ya ce Faransawa da Jamusawa da ke fuskantar hare haren ta’addanci za su fuskanci bincike kafin shiga Amurka idan har ya aka zabe shugaban kasa.

Talla

Trump ya fadi haka ne a wata tattaunawar da aka yi da shi a kafar yada labarai ta NBC a yau Lahadi.

Trump ya ce Faransa da Jamus matsaloli ne ga Amurka wadanda ke fuskantar hare haren Mayakan IS.

An tambayi Dan takarar ne ko zai takaita shigar baki daga Faransa, sai ya kada baki ya ce kasar na cikin damuwar hare haren ta’addanci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.