SYRIA

Syria: An kai wa Asibitoci hari a Aleppo

Asibitoci na fuskantar barazana a Syria
Asibitoci na fuskantar barazana a Syria Reuters/Youssef Boudlal

Jami’an kiwon lafiya a kasar Syria sun ce hare haren jiragen yakin sojojin gwamnatin Bashar Al Assad sun yi sanadiyar lalata wasu asibitoci na wucin gadi guda hudu a gabashin birnin Aleppo.

Talla

Wata Kungiyar bayar da agajin gaggawa mai suna “White Helmets” ta ce tun a ranar Asabar ake luguden wuta akan asibitocin wanda ya haifar da tarnaki ga sama da mutane 200,000 da ke matukar bukatar taimako.

Kungiyar agajin ta ce wani jariri mai kwanaki biyu a duniya ya rasa ransa a hare haren.

Kungiyar kuma ta bayyana fargabar fuskantar yunwa a garin Gazientip da ke kan iyakar Turkiya da Syria, kasancewar gidajen samar da abinci biyu ne kawai ke aiki yadda ya kamata a garin da ke da yawan mutane 300,000.

Yanzu haka sojan gwamnati sun shafe kwanaki 15 zagaye da gabashin birnin na Aleppo, a kokarin da suke yi na kwace birnin baki daya daga hannun yan tawaye.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.